logo

HAUSA

Kamaru ta kaddamar da gangamin fara riga kafin cutar COVID-19

2021-04-13 09:56:04 CRI

Kamaru ta kaddamar da gangamin fara riga kafin cutar COVID-19_fororder_新冠疫苗

Kasar Kamaru ta kaddamar da gangamin fara alluran riga kafin COVID-19 a jiya Litinin, bayan ta karbi kashin farko na alluran da Sin ta ba ta gudunmuwarsu a ranar Lahadi.

An fara bayar da riga kafin ne a wata cibiyar kula da masu cutar COVID-19 dake birnin Yaounde, inda ministan lafiya na kasar, Malachie Manaouda, ya kasance mutum na farko a kasar da ya karbi allurar.

Jim kadan bayan da aka yi masa allurar a gaban tarin jami’an gwamnati da ma’aikatan lafiya, ministan ya bayyana cewa, ya ji dadinta, kuma ba ta tattare da matsala, yana mai cewa allurar tana da aminci.

A cewarsa, aikin bayar da allurar zai mayar da hankali kan jami’an lafiya a zagaye na farko. Kana, zuwa yau Talata, za a samar da alluran ga dukkan yankunan kasar. (Fa’iza Mustpha)

Fa’iza Mustpha