logo

HAUSA

Kamaru za ta tsaurara matakan yaki da safarar bil adama

2021-04-08 10:22:30 CRI

Kamaru za ta tsaurara matakan yaki da safarar bil adama_fororder_3

Ministan walwala da jin dadin al’umma na jamhuriyar Kamaru, Pauline Irene Nguene, ya yi alkawarin ci gaba da daukar matakan kakkabe laifuffukan safarar bil adama da kuma hukunta duk wani jami’in gwamnati da aka samu da hannu wajen aikata muggun laifi.

Ministan ya yi alkawarin ne a lokacin wani taron da aka gudanar a Yaounde, babban birnin kasar, inda ya yi bayani kan wani rahoton bincike da aka gudanar na hadin gwiwar ma’aikatar da kungiyar makaurata ta kasa da kasa IOM game da halin da ake ciki dangane da masu aikata laifuffukan safarar bil adama a kasar ta tsakiyar Afrika.

A bisa binciken da aka gudanar, galibin mutanen da aka yi safararsu mata ne, da kananan yara da kuma mutane masu bukata ta musamman. Mutane da dama sun fada kangin bauta.

Nguene ya ce, kasar Kamaru za ta kaddamar da shirin gangamin wayar da kai domin dakile karuwar laifuffukan safarar bil adama.

Jami’an sun amince cewa, domin samun nasarar kawar da muggun laifin wanda ke jefa rayuwar mutanen da lamarin ya ritsa da su da iyalai da kuma al’umma cikin garari, aiki ne dake bukatar hadin gwiwar kasa da kasa.(Ahmad)