logo

HAUSA

Tallafin alluran rigakafin COVID-19 na Sin sun isa Kamaru

2021-04-12 13:23:59 CRI

Tallafin alluran rigakafin COVID-19 na Sin sun isa Kamaru_fororder_hoto

A daren ranar 11 ga wata, tallafin alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin hada magunguna na Sinopharm na kasar Sin, ya isa birnin Yaoundé, fadar mulkin kasar Kamaru. Wannan shi ne karo na farko da alluran rigakafin COVID-19 suka shiga cikin kasar, tun bayan barkewar wannan annoba.

Jakadan kasar Sin dake kasar Kamaru, Wang Yingwu ya bayyana cewa, alluran rigakafin kasar Sin suna da inganci da kuma aminci, wadanda kuma suke samun amincewar kasa da kasa, kana an yi imanin cewa, za su taimakawa kasar Kamaru wajen cimma nasarar yaki da cutar.  Ya ce kasar Sin tana cika alkawarinta, tana dukufa wajen raba alluran rigakafin cikin yanayin adalci, musamman ma ga kasashe masu tasowa. A cewar jakadan, a bana, ake cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Kamaru, kuma kasar Sin tana son hada gwiwa da kasar Kamaru wajen zurfafa hadin gwiwarsu a fanni kiwon lafiya da sauransu.

A nasa bangare kuma, firaministan kasar Kamaru Dion Ngute Joseph ya ce, kasarsa tana godiya matuka game da taimakon alluran rigakafi da kasar Sin ta samar mata, wanda ya nuna kyakkyawan zumuncin dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce alluran rigakafin cutar COVID-19 su ne dabara mafi amfani wajen yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, inda ya ce suna maraba da wannan allura a ko wane lokaci. Ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Kamaru za ta samar da alluran rigakafi ga al’ummomin kasar nan take, inda za a fara da ma’aikatan lafiya. (Maryam)