logo

HAUSA

Al’ummar Kamaru na shaukin karbar rigakafin COVID-19 da Sin ta tallawa kasar da ita

2021-04-09 14:16:18 CRI

Al’ummar Kamaru na shaukin karbar rigakafin COVID-19 da Sin ta tallawa kasar da ita_fororder_210409-Kamaru

Sakataren dindindin na shirin rigakafi da aka fadada a kasar Kamaru Shalom Tchoukfe Ndoula, ya ce alluran rigakafin cutar COVID-19 200,000 na kamfanin Sinopharm da kasar Sin ta baiwa Kamarun tallafin su, na kan hanyar isa kasar a ranar Lahadi.

Mr. Ndoula, ya ce rukunin farko na al’ummun kasar da za a yiwa rigakafin su ne ma’aikatan lafiya, da masu cututtuka masu tsanani, wadanda ke iya jefa su cikin hadarin harbuwa da cutar ta COVID-19. Bayan nan ne kuma, za a fadada shirin rigakafin zuwa sauran bangarorin al’ummar kasar baki daya.

A cewar Johnson Esunge, wani jami’i dake lura da wani dakin gwajin cututtuka a kasar, wanda ya gudanar da gwajin cutar da ya haura 10,000, zuwan rigakafin babbar nasara ce a yakin da Kamaru ke yi da wannan annoba.

Ya ce aiwatar da rigakafin zai taka muhimmiyar rawa, a kokarin da kasar ke yi na farfado da tattalin arziki, wanda ya sha matsi sakamakon ka’idojin ba da tazara da kulle, da suka gurgunta tsarin saye da sayarwa, tare da jefa ’yan kasar da dama cikin matsalar karancin ayyukan yi.  (Saminu)