logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Mayarwa Amurka Martani Kan Manyan Laifuka Biyar Na Keta Hakkin Dan Adam Da Take Aikatawa

2021-04-07 19:48:04 CRI

Kasar Sin ta mayarwa Amurka martani, bayan da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka ta tsaya kai da fata cewa, takunkumin da ta kakaba wa kasar Sin, ya dace wajen hana gwamnatin kasar Sin keta hakkin dan Adam da aikata kisan kiyashi a yankin Xinjiang.

Sai dai mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasa Sin, Zhao Lijian, ya karyata zargin, yana mai cewa, batun aikata kisan kiyashi, karya ce tsagwaranta.

Daga nan, sai ya zayyana “manyan laifuffuka biyar” da gwamnatin Amurka ta aikata a cikin karnin da suka gabata, kama daga kisan ‘yan asalin Indian a karni na 19 zuwa nuna wariyar launin fata da raba kan al’umma.(Ibrahim)

Ibrahim