logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Kare Sanarwar Da Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Turkiya Ya Wallafa A Shafin Tiwita Game Da Xinjiang

2021-04-07 19:26:26 CRI

A yau ne, kasar Turkiya ta kira jakadan kasar Sin dake kasar, bayan da ofishin jakadancin Sin da ke Turkiya ya bayyana a shafin Tiwita cewa, yana da “‘yancin mayar da martani” ga shugabannin adawa na Turkiya da suka zargi yadda kasar Sin take kula da musulmin Uygur dake yankin Xinjiang.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian, ya kare sanarwar da ofishin jakadancin Sin da ke Turkiya ya wallafa yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa. Yana mai cewa, ‘yan siyasar Turkiya, sun yi ta yin maganganu a shafin Tiwita game da ta’addanci, kuma hakan shiga hurumin mulkin kai da cikakkun yankunan kasar Sin ne, kuma matakin ya haifar da ra’ayi na nuna wariya.

Zhao ya bayyana cewa, wannan shi ne karon farko da ofishin jakadancin kasar Sin ya mayar da martani kan irin wannan sanarwa, kuma ya dace kwarai.

Ya ce, kasar Sin tana fatan Turkiya a matsayinta na kasar da ta dade tana fama da ayyukan ta’addanci da ‘yan aware, za ta dauki matakin da ya dace, idan ana maganar matsayin kasar Sin na kare ‘yancin kai da cikakkun yankunanta gami da matakan ta na yaki da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi.(Ibrahim)

Ibrahim