Ziyara zuwa jihar Xinjiang
2021-04-07 10:42:18 CRI
Kwanan nan, babban sakataren kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) Vladimir Imamovich Norov, tare da sauran wasu jami’an diplomasiyya na kasashe 21 da ke kasar Sin sun kai ziyara biranen Urumqi da Kashgar da Aksu na jihar Xinjiang, inda suka gane ma idanunsu ci gaban zaman takewar al’ummar wurin. A ganinsu, an samu gagaruman ci gaba ta fannin yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a wurin, ga kuma kwanciyar hankali ya tabbata.