logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya taya Nguyễn Xuân Phúc murnar zama shugaban Vietnam

2021-04-05 19:45:34 CRI

Yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wa Nguyễn Xuân Phúc sakon taya murnar zama shugaban kasar Vietnam.

A cikin sakonsa, Shugaba Xi ya ce, Sin da Vietnam suna makwabtaka da juna. Daga shekarar bara zuwa yanzu, suna taimakawa tare da mara wa juna baya, har sun samu kyakkyawan sakamako wajen dakile yaduwar cutar COVID-19. Kasashen 2 sun raya huldarsu yadda ya kamata, sun kuma bude wani sabon shafi na bunkasa kyakkyawar makwabta da zumunci a tsakaninsu.

Xi ya kuma jaddada cewa, kasashen duniya na fuskantar manyan sauyawa a halin yanzu. An shiga muhimmin lokaci wajen bunkasa hulda a tsakanin kasashen 2 da kuma ayyukan raya kasa ta gurguzu. Xi ya kara da cewa, yana sa muhimmanci kan ci gaban huldar da ke tsakanin Sin da Vietnam, yana kuma son hada kai da Nguyễn Xuân Phúc wajen kara azama kan raya huldar abokantaka da hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, a kokarin amfanawa kasashen 2 da al’ummominsu baki daya, bisa manufar samun makomarsu ta bai daya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan