logo

HAUSA

Wang Jie —— Jarumi a zuciyar Xi Jinping

2021-04-03 21:04:59 CRI

Wang Jie	—— Jarumi a zuciyar Xi Jinping_fororder_1

Bayan da aka kira babban taro karo na 18 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin har zuwa yanzu, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba shugaba Xi Jinping ya bayyana wasu labarai masu burgewa da suka jibanci jarumai ‘yan mazan jiya, don kira ga daukacin al’ummar kasar su tuna da mutanen da suka sadaukar da rayukansu ga kwato ‘yancin al’umma da samar musu rayuwa mai dadi. Akwai wani matashin soja a ciki, wanda ya sadaukar da ransa yana da shekaru 23 a duniya kacal. Kuma shugaba Xi Jinping ya bayyana shi a matsayin jaruminsa a zuciya.

Wang Jie	—— Jarumi a zuciyar Xi Jinping_fororder_2

A ranar 14 ga watan Yulin shekara ta 1965, a wani horon sojan da aka yi, Wang Jie ya gamu da hatsarin fashewar bom na ba zato ba tsammani, inda ya yi ruf da ciki kan bom din, don kare rayukan sauran sojoji da al’umma su 12. Inda ya sadaukar da ransa a yana da shekaru 23 kadai a duniya.

A ranar 13 ga watan Disamban shekara ta 2017, shugaba Xi ya ziyarci wata rundunar soja, inda ya gana da sojojin dake kungiyar kamfanin sojan da Wang Jie ke ciki lokacin da yake raye, har ya ziyarci nune-nunen rayuwarsa. Xi Jinping ya ce, ya san labarin Wang lokacin da yake karamin yaro, kuma shi jaruminsa ne.

Wang Jie	—— Jarumi a zuciyar Xi Jinping_fororder_3

Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta yi wa bataliyar Wang Jie lakabi da sunansa, wadda ke da tarihin shekaru sama da 50. A farkon shekara ta 2019, dukkan sojojin dake bataliyar sun gabatar da wasika zuwa ga shugaba Xi, inda suka bayyana ayyukan da suka yi, da aniyarsu na ci gaba da himmatuwa wajen kara samun nasarori.

Kana a cikin wasikar da Xi Jinping ya rubuto musu, ya bayyana fatansa gare su na ci gaba da nuna hazaka wajen inganta kwarewarsu a fannin aikin soja, don su zama nagartattun sojoji a sabon zamanin da muke ciki.(Murtala Zhang)