logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi jimamin mutuwar ‘yan kasarsa a hadarin jirgin kasar yankin Taiwan

2021-04-03 16:37:54 CRI

Xi Jinping, sakatare Janar na kwamitin koli na JKS, ya yi jimamin rashin ‘yan kasar da suka mutu cikin hadarin jirgin kasa da ya auku a yankin Taiwan jiya Juma’a.

Shugaba Xi ya yi matukar kaduwa da hatsarin da ya rutsa da mutane da dama, inda ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da jajantawa wadanda suka jikkata da kuma yi musu fatan samun sauki cikin sauri. (Fa’iza Mustapha)