logo

HAUSA

Mu tuna da shahidai tare da shugaba Xi Jinping

2021-04-02 16:59:12 CRI

Ranar 4 ga watan Afrilu na bana ita ce bikin share kaburbura da tunawa da magabata na kasar Sin, gabanin wannan rana, bari mu nuna girmamawa ga shahidai tare da shugaban kasar Sin Xi Jinping domin tunawa da tarihi.

Xi Jinping ya gabatar da Jawabi yayin taron murnar cika shekaru 95 da kafuwar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin da aka yi a shekarar 2016, domin tunawa da wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare kasar Sin.

Xi Jinping ya kai ziyara a dakin tunawa da yakin da aka yi a garin Siping a lokacin da ake neman ‘yantar da jama’ar kasar Sin tsakanin shekarar 1946 da ta 1948, a ranar 22 ga watan Yuli na shekarar 2020.

A ranar 20 ga watan Mayu na shekarar 2019, Xi Jinping ya kai ziyara dakin tunawa da wurin da aka fara doguwar tafiyar sojojin dake karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, dake gundumar Yudu na birnin Ganzhou, inda ya gana da iyalai na wasu shahidai.

A ranar 16 ga watan Satumba na shekarar 2019, Xi Jinping ya kai ziyara dakin tuna da shahidai na birnin Xinyang.

A ranar 20 ga watan Agusta na shekarar 2019, Xi Jinping ya ziyarci wurin tuna da jajayen sojojin Sin wato Red Army dake gundumar Gaotai na birnin Zhangye na lardin Gansu, inda ya aza furanni a gaban dutsen tunawa da shahidai.

A ranar 20 ga watan Mayu na shekarar 2019, Xi Jinping ya ajiye furanni a gaban wurin tunawa da fara doguwar tafiya da jajayen sojoji wato Red Army suka yi, a gundumar Yudu dake birnin Ganzhou.

A ranar 12 ga watan Satumba na shekarar 2019, Xi Jinping ya kai ziyara wurin tuna da juyin juya halin da aka yi don ‘yantar da jama’ar kasar Sin, dake yankin Xiangshan na birnin Beijing, inda aka tsara bikin nune-nune mai taken “aza harsashi ga kafuwar sabuwar kasa ta Sin”. (Maryam Yang)