logo

HAUSA

Lale shan kofi ba shi da nasaba da kamuwa da ciwon sankara

2021-02-14 08:04:41 CRI

Lale shan kofi ba shi da nasaba da kamuwa da ciwon sankara_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20171212_14eb1c54020440aab05c5a30ecb259ff.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

An dade ana takkadama kan illar da kofi ke haifarwa wa lafiyar dan-Adam. Amma wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Australiya ya shaida mana cewa, shan kofi ba shi da nasaba da batun kamuwa da ciwon sankara. Idan mutum ya sha kofi a ko wace rana, to, hakan ba zai kara ko kuma rage barazanar da suke fuskanta ta kamuwa da ciwon sankara ba.

Masu nazari daga kwalejin nazarin ilmin likitanci na Berghofer na kasar Australiya, sun kaddamar da rahoton nazari cikin mujallar ilmin cututtuka masu yaduwa ta kasa da kasa, inda suka nuna cewa, sun samu bayanan ne daga rumbun adana bayanan halittu na Birtaniya. wadannan bayanai sun shafi mutane dubu 46 wadanda suka kamu da cututtukan sankara mafi muni, a cikinsu kuma wasu dubu 7 sun rasa rayukansu sakamakon ciwon sankara. Masu nazarin sun kwatanta bayanan da suka shafi kwayoyin dabi’a halittunsu da al’adarsu ta shan kofi, da kuma bayanan da suka shafi mutane dubu 270 wadanda ba su taba kamuwa da ciwon sankara ba. A karshe dai, masu nazarin sun gano cewa, hakika shan kofi ba shi da nasaba da kamuwa da ciwon sankara. Idan mutum yana shan kofi a ko wace rana, to, hakan ba zai kara ko kuma rage barazanar da mutum ke fuskanta ta kamuwa da ciwon sankara ba.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, yawan kofi da wani yake sha a ko wace rana, ba shi da nasaba da yiwuwar kamuwa da wani nau’in ciwon sankara. Haka kuma, babu wata alaka a tsakanin shan kofi da kuma rasa rayuka sakamakon wani nau’in ciwon sankara.

Wannan nazari da aka gudanar a kasar Australiya ya shafi wasu nau’o’in cututtukan sankara da a kan kamu da su, alal misali ciwon sankaran mama, da na kwan mace, da huhu da na mafitsara. An gano cewa, babu wata alaka a tsakanin batun shan kofi da kuma raguwa ko karuwar yiwuwar kamuwa da wadannan cututtukan sankara. Amma duk da haka, yayin da masu nazarin suka yi binciken kan ciwon sankarar uwar hanji, ba su iya tabbatar da cewa, babu irin wannan alaka a tsakanin batun shan kofi da kuma kamuwa da ciwon sankarar uwar hanji ba. Suna ganin cewa, wajibi ne a ci gaba da yin nazarin a wannan fanni.

Akwai sinadaran Caffeine da Kahweol a cikin kofin da mu kan sha kullum. Nazarin da aka gudanar kan dabbobi ya shaida mana cewa, wadannan sinadarai, suna amfani wajen yaki da ciwon sankara. Amma ya zuwa yanzu ba a tabbatar da amfaninsu kan dan Adam ba tukuna.(Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan