logo

HAUSA

Gianni Infantino: Dage lokacin buga gasar cin kofin kulaflikan duniya matakin nuna goyon baya ne

2020-12-25 10:07:38 CRI

Gianni Infantino: Dage lokacin buga gasar cin kofin kulaflikan duniya matakin nuna goyon baya ne_fororder_FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce an dage buga gasar cin kofin kulaflika 24, wanda a baya aka shirya gudanarwa a kasar Sin a shekarar 2021, zuwa wani lokaci nan gaba, a wani mataki na nuna goyon baya ga kulaflikan kasashe daban daban, na samun damar buga gasannin cikin gida yadda ya kamata.

Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, ya bayyana cewa, ko shakka ba bu, wannan gasa za ta kayatar, idan lokacin buga ta yayi. Infantino ya yi wannan tsokaci ne yayin taron hukumar kwallon kafa ta nahiyar Asiya AFC, wanda ya gudana ta kafar bidiyo a farkon makon jiya.

FIFA tana fatan baiwa kulaflikan sassan duniya daban daban damar buga manyan gasanni kamar na UEFA, da gasar zakarun turai, da gasar Copa America, gasannin da a baya aka tsara gudanarwa a bana, amma bullar cutar COVID-19 ta sanya dole aka dade su.

Infantino ya ce, sabuwar gasar kulaflika ta hukumar FIFA za ta gudana a kasar Sin kamar yadda aka tsara tun da fari, yana kuma fatan za a kai ga sanya sabon lokacin buga gasar nan ba da jimawa ba.

Gasar wadda aka karawa yawan kungiyoyi mahalarta, za ta karbi bakuncin Karin kulaflika daga nahiyar Asiya, da wasu kungiyoyi na sauran nahiyoyin duniya.

A watan Oktoban bara, FIFA ta yanke shawarar shirya sabuwar gasar kulaflika ta duniya da aka yiwa kwaskwarima, wadda za ta kunshi kungiyoyi 24, wato za ta maye gurbin wadda ake bugawa tsakanin kungiyoyi 7 a baya. Bayan dage sabuwar gasar, an zabi Japan a matsayin kasar da za ta karbi bakuncin gasar kungiyoyin kasa da kasa ta 2021 a watan Disamabar badi, yayin da gasar 2020 kuma za a buga ta a Qatar cikin watan Fabarairun 2021.

Yayin taron hukumar ta AFC, shugaban ta Shaikh Salman bin Ebrahim Al Khalifa, ya jinjinawa iyalin kwallon kafar nahiyar Asiya, bisa yadda suka tunkari yanayi mafi wahala a bana "wato shekara da AFC ba ta taba ganin irin ta ba a tarihin kwallo".

Shaikh Salman bin Ebrahim Al Khalifa ya ce "Cikin wannan yanayi mafi sarkakiya mai wuyar sha’ani, AFC sun ci gaba da tsara manufofi, da tsayawa kan ingantattun kudurorin da aka sanya gaba. Tabbas, akwai kalubale. AFC ita ce hukuma ta farko da ta sanar da dage buga wasanni yayin da annobar COVID-19 ta barke, hukumar ta nuna karfin hali, ta kuma nace ga bin manufofin kare rayukan al’umma yadda ya kamata.

Yayin taron na AFC na wannan karo, hukumar kwallon kafa ta Tsibirin Northern Mariana ko NMIFA, ta zama ta 47 da ta kasance memba a hukumar AFC.