logo

HAUSA

Namibia ta sha kashi a hannun Mali a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka na 2021

2020-11-18 16:17:01 CRI

A jiya ne kasar Namibiya ta sha kashi a gida a hannun kasar Mali da ci biyu da 1, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafan nahiyar Afirka da za a fafata a shekarar 2021.

Da wannan sakamako, kasar Namibiya ta kasance ta uku a rukuni na 1 wato A, da maki uku, bayan buga wasanni hudu. Nan gaba ne kuma za ta ziyarci kasar Chadi, sai kuma daya wasan da za ta buga da Guinea a gida.

Yanzu dai kasar Malin ce ke kan gaba a rukinin nasu da maki 10, sai kasar Guinea dake biye mata baya da maki 8, yayin da Chadi ke ta karshe a rukinin da maki 1 kacal.

Kocin Namibiya Bobby Samaria ya bayyana cewa, bai ji dadin wannan sakamako ba, amma ya ce tawagarsa za ta ci gaba da yin kokari har sai ta samu nasara.(Ibrahim)