logo

HAUSA

Kasar Sin ta tura kashin farko na gudummawar alluran riga kafin COVID-19 zuwa Afirka

2021-02-09 23:20:39 CRI

A gobe da safe agogon kasar Equatorial Guinea, ake saran kashin farko na gudummawar alluran riga-kafin COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Equatorial Guinea zai isa Malabo, babban birnin kasar.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan Talatar nan yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, ya ce wannan shi ne kashin farko na tallafin riga-kafin COVID-19 da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka. Wannan ya nuna alkawarin da kasar Sin ta yi tun farko cewa, da zarar ta samar tare da fara amfani da rigakafin, to zai zama kayan daukacin al’ummar duniya.

Wang Wenbin, ya ce a shirye kasarsa take ta yi aiki da kasashen Afirka, ciki har da Equatorial Guninea, wajen gudanar da hadin gwiwar samar da riga kafi, da baiwa kasashen Afirka goyon baya da taimako bisa bukatunsu, gwargwadon karfinta. Haka kuma kasar Sin za ta yi aiki tare da kasashen na Afirka wajen yakar annobar, da yayata samun ci gaba tare bayan yakar annobar da kuma amfanawa al’ummomin kasashen Sin da Afirka.(Ibrahim)