logo

HAUSA

UNEP tace inganta tsafta zata taimakawa Afirka farfadowa daga annoba cikin hanzari

2021-02-03 10:17:37 CRI

Babbar jami’ar shirin kare muhalli ta MDD UNEP, ta ce ya kamata dukkan kasashen Afrika su mayar da hankali wajen zuba jari a fannin tsaftar muhalli da tsaftace gurbataccen ruwa a matsayin wani bangare da zai taimaka musu wajen farfadowa daga annobar COVID-19.

Leticia Carvalho, shugabar sashen kula da harkokin teku da samar da ruwa mai tsafta na hukumar kula da muhalli ta MDD(UNEP), ta ce bunkasa samar da kayayyakin tsafta a Afrika zai taimakawa nahiyar wajen cimma burinta na samun cigaba a daidai lokacin da ake fama da rashin tabbas sakamakon barkewar annoba.

Jami’ar ta ce, a yayin da duniya ke neman hanyoyin farfadowa mafiya inganci bayan kawo karshen annobar COVID-19, fifita batun tsaftace gurbataccen ruwa da inganta samar da muhimman ababen tsaftar muhalli a Afrika yana da matukar muhimmanci. Carvalho ta bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da shirin kula da tsaftar muhalli da tsaftace ruwan dagwalo na Afrika wanda hukumar UNEP tare da hadin gwiwar bankin bunkasa cigaban Afrika AfDB suka shirya.

A bisa kididdigar da shirin ya gabatar, sama da rabin al’ummar kasashe 34 daga 38 da ke kudu da hamadar Sahara suna fuskantar karancin hanyoyin samun muhimman kayayyakin wanke hannu.

Carvalho tace, kasashen Afrika zasu iya cimma nasarar kudiri na 6 na ajandar SDG na samar da dawwamamman cigaba nan da shekarar 2030 wanda ya shafi batun samar da tsaftaccen ruwa da inganta tsaftar muhalli da zummar bunkasa hanyoyin samun kudade da manufofin cigaba.(Ahmad)