logo

HAUSA

Taron ministocin kasashen Afirka zai mayar da hankali kan COVID-19 da AfCFTA

2021-02-04 10:04:05 CRI

Darekta mai kula da dunkulewar shiyya da cinikayya a hukumar hukumar MDD mai kula da harkokin tattalin arzikin Afirka(UNECA) Stephen Karingi, ya bayyana cewa, taron ministocin kudi, tsare-tsare da raya tattalin arziki na kasashen Afirka, karkashin hukumar dake tafe, zai mayar da hankali ne kan yarjejeniyar cinikayya maras shige ta nahiyar Afirka da kuma annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar wasu sassan duniya.

Darektan ya ce, taken taron ya zo kan gaba, ta yadda zai kasance wani dandali da ministoci da masana za su tattauna bukatar tabbatar da ganin, an hade matakan raya fasahohin zamani da masana’antu cikin manufofi da tsare-tsaren zamanantar da masana’antun kasashen nahiyar.

A cewar hukumar ta UNECA, fara aiki da yarjejeniyar cinikayya maras shige ta Afirka, ya nuna kudirin nahiyar na zamanantar da masana’antu, yayin da harkar cinikayya ta yanar gizo, dake zama jigon zamanantar da tattalin arzikin nahiyar, ke zama ginshikin farfado da ababan more rayuwa.

Taken taron wanda zai gudana ta kafar bidiyo daga ranar 17 zuwa 23 ga watan Maris, shi ne “dorewar zamanantar da masana’antun Afirka da fadada hanyoyi a zamanin da ake cin gajiyar fasahar zamani, a yayin da ake fama da annobar COVID-19”.(Ibrahim)