logo

HAUSA

Kasashen duniya na sa ran gudunmawar da Sin za ta bayar wajen warware kalubalen da duniya ke fuskanta

2021-01-25 11:02:29 CRI

Za a kira taron ajandar Davos na dandalin tattauna kan tattalin arzikin duniya daga yau 25 zuwa 29 ga wata ta kafar bidiyo. Bisa gayyatar da wanda ya kafa dandalin kuma shugaban gudanarwa Klaus Schwab ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron, kuma zai ba da jawabi ta bidiyo a yau Litinin.

A watan Jarairun shekarar 2017, shugaba Xi ya halarci taron shekara-shekara na dandali karo na farko tare da ba da jawabi mai taken “Sauke nauyin dake wuya cikin hadin kai don ingiza bunkasuwar duniya baki daya”. A cikin jawabin, shugaba Xi ya bayyana ra’ayi da matakan da Sin take dauka kan dunkulewar tattalin arzikin duniya tare da nuna boyon bayan mai karfi ga wannan ajanda.

Babban diraktan dandalin Børge Brende ya nuna cewa, jawabin da shugaba Xi ya bayar yau shekaru 4 da suka gabata na da babbar ma’ana, wanda kuma ya ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya cikin wata hanya da ta dace da ingiza warware kalubalen da duniya ke fuskanta wajen samun bunkasuwar tattalin arziki.

A ganin manazartan kasa da kasa, ci gaban tattalin arziki da Sin take samu duba da koman bayan sauran kasashe saboda cutar COVID-19 dake ci gaba da addabar duk fadin duniya, zai karawa sauran kasashe kwarin gwiwa. Mai nazarin batutuwan kasar Sin na kasar Brazil Ronnie Lins ya ce, Sin tana kan matsayi mai muhimmanci a cikin tattalin arzikin duniya. Saurin farfadowar tattalin arzikinta zai yi amfani ga saurin farfadowar tattalin arzikin sauran kasashe. Duk duniya na fatan Sin za ta gaggauta samun farfadowar tattalin arzikinta, don ta ba da jagoranci ga tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)