logo

HAUSA

Jawabin da Xi ya yi a taron Davos a shekarar 2017 ya amsa yadda za a farfado da tattalin arziki bayan annoba

2021-01-15 21:19:24 CRI

A taron Davos da aka yi a watan Janairu na shekarar 2017, Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken “daukar alhaki cikin hadin gwiwa domin raya kasashen duniya”. A jawabinsa, Xi ya ce, gabanin ra’ayin kariyar ciniki, kasashen duniya sun nuna rashin tabbas kan bunkasuwar tattalin arziki. Kuma gamayyar kasa da kasa na fatan kara karfin kasashen duniya wajen tafiyar da harkokin duniya yadda ya kamata.

Xi, ya yi musayar ra’ayoyi da mahalarta taron tattalin arzikin duniya, inda ya ce, “ya kamata mu tsaya tsayin daka wajen raya tattalin arzikin duniya bisa ka’idar bude kofa ga waje, domin samar da damammaki da cimma moriyar juna.” Wannan shi ne dabarar da Xi ya gabatar wa kasashen da ba su da dabarun raya tattalin arzikinsu.

Haka kuma, ya yi kira ga kasa da kasa da su inganta aikin gina yankin ciniki cikin ‘yanci na yankin Asiya da Pasific, da gaggauta shawawarin kulla dangantakar abokantaka ta tattalin arziki a dukkanin fannoni na yankin, domin bullo da wani tsarin ciniki cikin ‘yanci da zai tallafawa kasashen duniya

Yaduwar annobar cutar COVID-19 ya kawo barazana ga kasashen duniya, amma, kamar yadda Xi Jinping ya ce, duk wani kalubalen da muke fuskanta, ba zai hana mu samun ci gaba ba, kuma, tabbas, za mu fito da wata hanya. Domin ra’ayinmu na kara bude kofa ga waje da yin hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban ba zai taba canjawa ba. (Maryam)