logo

HAUSA

DAVOS na fatan sauraron murya daga kasar Sin

2020-01-23 14:04:19 cri

Za a kira taron shekara-shekara na DAVOS na 2020 daga ranar 21 zuwa 24 mai jigon "Hadin kan duniya don samun ci gaba mai dorewa". Ana sa ran sauraron murya daga kasar Sin.

Mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng, wanda ya taba halartar taron ya nuna cewa, hanya da ta dace da za a bi wajen magance wahalhalu da matsaloli da ake fuskantar, a bangaren dunkulwar tattalin arzikin duniya bai daya ita ce, kafa tsarin duniya mai bude kofa, da yin hakuri da juna, kuma abu mafi muhimmanci shi ne, nacewa ga gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban.

An ce, wannan hanya ta kasance mataki dake bayyana ruhin jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi, a taron shekaru 3 da suka gabata, kuma ya bayyana cewa, Sin na tunani da nazari mai zurfi, kan sauye-sauyen yanayin duniya dake da ma'ana sosai.

Kaza lika Sin ta yi kira ga kasashe daban-daban, da su nace ga sulhuntawa cikin adalci, da taimakawa juna, da hadin gwiwa, don tinkarar kalubaloli tare, ta yadda za a ingiza tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya na bai daya, da bin hanyar kara bude kofa, da yin hakuri da juna, da amfanawa kowa, da samun daidaito da cin moriyar tare, ta yadda jama'ar kasa da kasa za su more ci gaban dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya, da bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Wannan ita ce shawarar Sin ga duniya, kuma ka'idar da Sin ta dade tana aiwatarwa, in ji jami'in kasar Sin. (Amina Xu)