logo

HAUSA

Xi zai halarci taron Davos

2021-01-19 16:06:39 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) da ake shiryawa a birnin Davos, wanda za a gudanar a ranar 25 ga watan Janairu ta kafar bidiyo.

Madan Hua ta sanar da cewa, shugaba Xi zai halarci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi bisa gayyatar Klaus Scwab, mutumin da ya kirkiro kuma shugaban dandalin na WEF. (Ibrahim)