logo

HAUSA

MDD ta yi tir da harin kunar bakin wake da aka kai Iraq

2021-01-22 12:21:58 CRI

MDD ta yi tir da harin kunar bakin wake da aka kai Iraq_fororder_1127010660_16112391854241n

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da munanan tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan fararen hula a wata kasuwar dake birnin Baghdad na Iraq a jiya Alhamis.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, Antonio Guterres, ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su tare da gwamnati da al’ummar Iraq, sannan ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Sakatare Janar din ya nemi al’ummar kasar su bijirewa duk wani yunkuri na jefa su cikin fargaba da tashin hankali da ke da nufin tauye zaman lafiya da kwanciyar hankali da hadin kan kasar. Ya kuma yi kira ga gwamnatin kasar ta tabbatar da ganowa tare da hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata munanan laifuka.

Har ila yau, ya jaddada kudurin MDD na marawa al’umma da gwamnatin Iraq baya, a kokarin da suke na karfafa zaman lafiya a kasar. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha