logo

HAUSA

Iraqi ta gabatar da sakamakon yaki da ta'addanci

2020-04-22 11:11:51 cri

Jiya Talata, hukumar tsaron kasar Iraqi ta sanar da cewa, daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa ranar 15 ga watan Afrilun bana, rundunar sojojin tsaron kasar, da hukumomin yaki da ta'addanci da rundunar 'yan sanda da ma sauran sassan kasar sun dauki matakan soja sau 1060 kan kungiyoyin ta'addanci dake cikin kasar, inda suka kashe 'ya'yan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi 135, tare da kwasar makamai da yawa.

Haka kuma, wannan aiki ya haddasa rasuwar jami'an rundunar sojojin tsaron kasar 88, yayin da mutane 174 suka jikkata, sa'an nan kuma, akwai fararen hula 82 da suka rasu, yayin da 120 suka ji raunuka. (Maryam)