logo

HAUSA

Abubuwan fashewa sun lalata wurin ajiye makamai a kusa da babban birnin Iraqi

2020-07-27 10:29:36 cri

Rundunar sojojin Iraqi ta sanar da cewa wasu abubuwan fashewa masu yawan gaske da suka fashe a ranar Lahadi sun lalata runbun ajiye makamai a sansanin sojoji dake kudancin Bagadaza, babban birnin kasar Iraqi.

An gano cewa, wurin ajiye makaman mallakin 'yan sandan gwamnatin tarayya ya fashe ne sakamakon tsananin zafi da kuma rashin ingancin wajen ajiyar, kamar yadda ofishin yada labaran dakarun tsaron hadin gwiwa na kasar Iraqin ya bayyana cikin wata sanarwa.

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Saad Maan, ya fadawa kafar yada labarai ta al-Iraqiya channel cewa, sama da motocin kashe gobara na hukumar tsaron fararen hula 20 ne suka kai dauki wajen domin kashe wutar da ta tashi, inda suka yi nasarar shawo kan kashi 70 bisa 100 na gobarar.

Rahotannin farko sun nuna cewa, wutar ta fara tashi ne a cikin wasu motoci dake dauke da tsoffin makamai kafin daga bisani wutar ta bazu zuwa sansanin, Maan ya kara da cewa, tuni ministan harkokin cikin gidan kasar Othman al-Ghanmi, ya ba da umarnin gudanar da bincike don gano musabbanin hadarin.(Ahmad Fagam)