logo

HAUSA

Za a sake hana fita da dare a Iraqi yayin bikin babbar Sallah

2020-07-27 11:06:46 cri

Gwamnatin kasar Iraqi ta yanke shawarar sake hana fita da dare a lokacin bikin babbar Sallah don hana saurin yaduwar annobar cutar COVID-19.

Kwamitin kiwon lafiya da tsaron kasar Iraqi wanda ya ba da sanarwar a jiya, ya ce yayin bikin babbar Sallah daga ranar 30 ga watan Yuli zuwa 9 ga watan Agusta, Iraqi za ta hana fita da dare. Kuma yuwuwar ci gaba da wannan tsari bayan bikin, ya dogara da halin da za a kasance ciki. Kana za a yarda da asibitoci masu zaman kansu su koma aiki bisa tanadin matakan kandagarki. Ban da wannan kuma, rundunar tsaron kasar za ta sa ido kuma tana da ikon neman tara daga wadanda suka sabawa dokar kandagarki.

Hukumar kiwon lafiya ta kasar ta ba da kididdiga a jiyan cewa, karin mutanen da suka kamu da cutar a wannan rana ya kai 2459, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar kuma, ya kai 110032, sannan yawan mamata ya kai 4362 wanda karin mamata a wannan rana ya kai 78. (Amina Xu)