MDD ta yi kira da a gaggauta tallafawa ‘yan gudun hijirar Habasha
2020-12-23 12:34:31 CRI
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, tare da wasu hukumomin jin kai 30, sun bukaci tallafin dalar Amurka miliyan 156, domin cimma muhimman bukatun jin kai na ‘yan gudun hijirar Habasha dake tserewa rikicin yankin Tigray, a rabin farkon shekarar 2021.
Ana sa ran tallafin zai kuma karfafa shirin karbar ‘yan gudun hijira a wasu kasashen yankin, idan aka samu karuwarsu.
Rikicin da aka shefe makonni ana yi a jihar Tigray dake arewacin Habasha tsakanin ‘yan tawaye da dakarun gwamnati, ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da raba wasu dubbai da matsugunansu, tare kuma da sanya miliyoyi cikin tsananin bukatar taimako.
A cewar hukumar ta MDD, cikin makonni 6 da suka gabata, sama da ‘yan gudun hijira 52,000 ne suka tsere daga Tigray zuwa gabashin Sudan. (Fa’iza Mustapha)
Labarai Masu Nasaba
- Tawagogin manazarta daga MDD za su shiga yankin Tigray na Habasha
- Sudan da Habasha sun amince hadadden kwamitin kula da iyaka na kasashen biyu su koma tattaunawa
- Firaministan Habasha: fadan da ya barke a kan iyakar Habasha da Sudan ba zai lalata dangantaka mai tarihi dake tsakaninsu ba
- MDD: Sama da mutum 63,000 suka tserewa gidajen su a Tigray