Sudan da Habasha sun amince hadadden kwamitin kula da iyaka na kasashen biyu su koma tattaunawa
2020-12-21 09:48:39 CRI
Kasashen Sudan da Habasha, sun amince hadadden kwamitin kula da iyaka na kasashen biyu su koma teburin tattaunawa a ranar 22 ga wata, a daidai lokacin da yankin iyakar kasashen ke fuskantar matsalar tsaro
A cewar wata sanarwa, Firaministan Sudan Abdallah Hamdok da takwaransa na Habasha, Abiy Ahmed, sun tattauna a gefen taron kungiyar raya kasashen gabashin Afrika IGAD, wanda aka fara jiya Lahadi, a Djibouti.
Kwamitin na hadin gwiwa ya yi taro na karshe ne a watan Mayun bana a birnin Addis Ababa na Habasha.
A ranar Laraba da ta gabata ne rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa, sojojin Habasha da tsageru, sun yi wa wani sansanin soji kwantar bauna a cikin yankin Sudan dake kan iyakar kasashen biyu.
Da ma a kan samu hare-haren tsageru a kan iyakar Sudan da Habasha a lokacin da ake shirin fara aikin gona. (Fa’iza Mustapha)