logo

HAUSA

MDD: Sama da mutum 63,000 suka tserewa gidajen su a Tigray

2020-12-16 11:54:11 CRI

MDD: Sama da mutum 63,000 suka tserewa gidajen su a Tigray

Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric ya ce sama da mutum 63,000 ne tashe tashen dake aukuwa a yankin Tigray na kisar Habasha ya raba da muhallansu, kuma MDD na fatan tantance hakikanin yawan su, da zarar jami’an ta sun samu ikon shiga yankin.

Stephane Dujarric, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin zantawa da  manema labarai, yana mai cewa MDD na ci gaba da tuntubar bangaren gwamnatin Habasha, don tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai ga yankin. A hannu guda kuma, jami’an MDD dake aiki a Sudan mai makwaftaka da Habashan, sun ce har yanzu suna fuskantar kalubale, game da taimakawa ‘yan gudun hijirar Tigray dake yunkurin tsallaka iyakar Habasha.

Bugu da kari, ana fuskantar karancin ruwan sha da kayan tsaftar muhalli, a cibiyoyin yada zango, da sansanin Um Raquba, mai karbar ‘yan gudun hijira sama da 16,000 da aka sake tsugunarwa.

Sama da mutane 50,000 ne suka tsere zuwa Sudan, tun bayan barkewar tashin hankali a Tigray a farkon watan Nuwamba, lokacin da ‘yan tawayen yankin suka fara dauki ba dadi da dakarun gwamnatin tarayyar Habasha, lamarin da ya katse shigar muhimman kayayyakin bukatar fararen hula, kuma hakan ya tilasawa dubun dubatar al’ummun yakin yin hijira, a gabar da kuma ake fama da karancin ababen bukata na yau da kullum, a sansanonin karbar ‘yan gudun hijirar.  (Saminu)

Saminu Alhassan