Firaministan Habasha: fadan da ya barke a kan iyakar Habasha da Sudan ba zai lalata dangantaka mai tarihi dake tsakaninsu ba
2020-12-20 15:58:35 CRI
Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed, ya sanar a ranar Asabar cewa, tashin hankalin da ya barke a baya bayan nan a kan iyakar Habasha da Sudan ba zai taba wargaza dadaddiyar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ba.
A bayanin da ya wallafa a shafinsa na twita, Ahmed ya ce, gwamnati tana cigaba da bibiyar halin da ake ciki game da batun dakarun tsaron kasar dake kan iyakar Habasha da Sudan. Ya jaddada cewa, wadannan al’amurra ba za su taba lalata dangantakar da aka kulla tsakanin kasashen biyu ba, kasancewa a ko da yaushe suna amfani da hanyoyin tattaunawa domin warware batutuwan dake shafarsu.
Ya kara da cewa, masu neman ruruta wutar rikici a tsakanin kasashen ba su fahimci hakikanin kakkarfar dangantaka mai cike da tarihi dake tsakanin bangarorin biyu ba.
A ranar Laraba, sojojin kasar Sudan sun bayyana cewa mayakan kasar Habasha sun kaddamar da hari kan dakarun Sudan dake kan iyakar kasashen biyu. (Ahmad Fagam)