logo

HAUSA

Sudan ta jaddada goyon bayanta ga shugabanci AU dangane da batun madatsar ruwan Nilu na Habasha

2020-12-15 15:37:44 CRI

Firaministan Sudan, Abdalla Hamdok, ya nanata goyon bayan kasarsa ga shugabancin Tarayyar Afrika, dangane da batun katafariyar madatsar ruwa ta Habasha.

Sudan da Habasha na tattaunawa game da dawowar Sudan din teburin sulhu, bayan Ministan kula da noman rani na Habasha, ya isa birnin Khartoum a jiya.

Sudan ta yanke shawarar kin shiga taron ministoci da aka yi kan batun madatsar ruwan a ranar 21 ga watan Nuwamba.

Sudan dai, na neman batun ya zarci matakin tattaunawa tsakanin ministoci, ya koma tsakanin shugabannin kasashen 3, sannan a ba masu sa ido daga Tarayyar Afrika da Amurka, matsayin masu shiga tsakani, sauyin da Masar da Habasha ba su gamsu da shi ba.

Habasha, wadda ta fara ginin madatsar ruwan a shekarar 2011, na sa ran samar da lantarki mai karfin megawatt 6,000 daga aikin, yayin da Masar da Sudan, da suka dogara da kogin wajen samun ruwan sha, suke fargabar madatsar ruwan za ta iya illata albarkatun ruwa. (Fa’iza Mustapha)