logo

HAUSA

An fara aikin ginin hedkwatar hukumar dakile cutuka ta Afrika CDC a Habasha bisa tallafin kasar Sin

2020-12-15 12:20:30 CRI

A ranar Litinin aka fara aikin ginin hedkwatar hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika wato Afrika CDC, wanda kasar Sin take taimakawa a birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a matsayin wani bangare na karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin kula da lafiyar al’umma.

Aikin mai cike da tarihi, ya shafi yanki mai fadin murabba’in mita 90,000 da kuma fadin ginin kusan 40,000, ana sa ran kammala aikin nan da watanni 25 masu zuwa. Za a samar da kayayyakin amfanin ofisoshi na zamani, da manyan dakunan gwaje gwaje, da sauran kayayyaki.

Idan aikin ya kammala, hedkwatar hukumar ta Afrika CDC za ta kasance wani muhimmin sashe mai cike da tarihi a babban birnin kasar ta Habasha, inda a can ne hedkwatar kungiyar tarayyar Afrika AU take, wanda kasar Sin ta taimakawa gina ta, a yanzu haka shi ne gini mafi tsawo a kasar Habasha.(Ahmad)

Ahmad Fagam