logo

HAUSA

Antonio Guterres ya nuna damuwa kan halin da ake ciki a yankin Tigray na Habasha

2020-12-08 11:38:49 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, a jiya Litinin ya bayyana damuwa matuka game da halin da ake ciki yanzu a yankin Tigray na kasar Habasha, inda dakarun gwamnati ke fafatawa da mayakan ‘yan tawayen yankin.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, jami’in na MDD ya ce, wajibi ne a gaggauta dawo da doka, da kare hakkoki na bil-Adam, da farfadowa da zai kunshi kowa da kowa, da kiyaye yanayin zamantakewa, da sake dawo da harkoki da hidima, da bude hanyoyin kaiwa ga masu bukatar taimakon jin kai.

Ya kuma nanata kudirin MDDr na goyon bayan yunkurin kungiyar tarayyar Afirka, da samar da taimakon jin kai ga ‘yan gudun hijira, da wadanda rikicin ya raba da muhallansu gami da daukacin mutanen dake cikin matsi .(Ibrahim)

Ibrahim Yaya