in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chen Xu:Yankin Xinjiang ya samu gagarumin ci gaba sakamakon zaman lafiyan da aka samu
2019-07-05 15:36:10 cri
Shugaban tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu ya bayyana cewa, yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin, ya samu gagarumin ci gaba ne, karkashin zaman lafiyar da aka samu.

Jami'in ya bayyana hakan ne, yayin da yake jawabi a gefen taron da aka shirya ranar Laraba mai taken " Ci gaban kare hakkin dan-Adam a yankin Xinjiang na kasar Sin", inda ya shaidawa mahalarta taron cewa, yankin yana samun ci gaba cikin sauri da zaman lafiyan da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba.

Chen ya ce tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018, an fitar da mutane miliyan 2.3 a yankin daga talauci, kana an baiwa dukkan kananan kabilu 'yancin yin addini da na al'ada, da 'yancin yin amfani da harsunan da ake magana da wadanda ake amfani da su wajen yin rubuta. Cikin sama da shekaru uku kuma, ba a taba aikata wani harin ta'addaci a yankin ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China