in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu gabatar da shirin CGTN da FBN sun tattauna batun takaddamar ciniki
2019-05-30 11:01:44 cri

A safiyar yau Alhamis, bisa agogon Beijing, mai gabatar da shiri a gidan telabijin na kasar Sin CGTN Malama Liu Xin, da takwararta ta gidan telabijin din FBN na kasar Amurka, Malama Trish Regan, sun yi musayar ra'ayi a wani shiri na FBN fuska da fuska, dangane da batun takaddamar ciniki da ake samu tsakanin Sin da Amurka.

A cikin shirin, Trish Regan ta tambayi Liu Xin, dangane da ra'ayinta game da shawarwarin da ake yi tsakanin Sin da Amurka, don daidaita takaddama da ciniki, inda Malama Liu ta amsa cewa, ba ta da majiya a cikin hukumomin kasashen 2, don haka ba ta san ainihin matsayin da aka cimma wajen gudanar da shawarwarin ba. Duk da haka tana ganin cewa gwamnatin kasar Sin ta riga ta bayyana matsayinta sarai.

Game da batun ikon mallakar fasahohi, Madam Liu ta ce, idan za a iya amfanar juna, da koyon fasahohin juna, to, babu matsala a ba da damar sayen ikon mallakar fasahohi. Ta haka kowa zai samu moriya. Liu ta yi amfani da wani misali wajen bayyana ra'ayinta, ta ce dadilin da ya sa ta iya Turancin Ingilishi shi ne, domin tana da wata malama ba'amurkiya wadda ta koyar da ita yaren.

Sa'an nan dangane da yadda wasu mutane ke son ganin kasar Sin ta yi watsi da matsayinta na wata kasa mai tasowa, Liu Xin ta ce, kasar Sin bata son zama kan tsohon matsayinta na wata kasa maras karfi, kuma tana son samun ci gaba, amma wani abu mai muhimmanci shi ne, yadda ake fahimtar kalmar "wata kasa mai tasowa". (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China