in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shin da gaske Amurka ba ta da kunya?
2019-05-17 19:36:39 cri

MDD ta ce, a matsayinta na kasa ta biyu da ta fi biyan kudin karo-karo da ake bukata domin tafiyar da harkokin MDD, kasar Sin ta riga ta biya dukkan kason kudadenta da yawansa ya kai kashi 12.01 cikin dari bisa lissafin MDD na yau da kullum. Dangane da hakan, Stefan Dujarrik, kakakin babban sakataren MDD ya bayyana godiyarsa cikin Sinanci da cewa, XieXie a yayin taron manema labaru.

Gwargwadon yadda kasar Sin ta sauke wannan nauyi, mene ne kasar Amurka, wadda a ganinta, ta fi kowa karfi a duniya, kuma ta fi biyan kudin da ake bukata domin tafiyar da harkokin MDD? Ya zuwa ranar 1 ga watan Janairun bana, ana bin Amurka kudin da ya kai dala miliyan 381 a lissafin gudanarwar MDD na yau da kullum, da kuma dalar Amurka miliyan 776 a fannin shimfida zaman lafiya. António Guterres, babban sakataren MDD ya nuna cewa, yawan kudin da ake bin Amurka ta fuskar kiyaye zaman lafiya ya zarce kashi 1 cikin kashi 3 bisa jimilar kudin da ake bi na tafiyar da harkokin.

An raba kudin karo-karo da ake bukatar kasashe su bayar domin tafiyar da harkokin MDD ne bisa karfin kasashe mambobin MDD. A kan yi la'akari da yawan GDP na kasa bisa karfin tattalin arzikin duniya cikin shekaru 3 zuwa 6 da suka wuce, matsakaicin yawan kudin shiga da dai sauransu.

Ya zuwa yanzu, jimilar tattalin arzikin Amurka ya kai dala triliyan 20, wanda ya kai kashi 24 cikin dari na dukkanin jimilar kasashen duniya, yawan kudin shigan ko wane mutum ya haura dubu 60. Saboda ganin haka, ya kamata ta biya kashi 22 cikin dari na kudin gudanar da harkokin MDD da kuma kashi 28 cikin dari na kudin kiyaye zaman lafiya, amma Amurka ta dade ba ta biya kudin tafiyar da harkokin MDD ba, har ma ta neman a rage biya irin wannan kudi ba gaira ba dalili, har ma ta kawo cikas ga harkokin MDD da aikin kiyaye zaman lafiya, matakin da ya sa suna da mutuncin Amurka sun zube a idon duniya saboda rashin tabuka komai.

Hakika Amurka tana da karfin biyan kudin da ake bukata don gudanar da harkokin MDD, dalilin da ya sa ta dauki wannan mataki shi ne, Amurka ta tozarta hukumomin kasa da kasa, ciki har da MDD, kuma Amurka ta yi amfani da tsarin sulhuntawa tsakanin bangarori daban-daban yadda take so, matakin da ya bayyana tunanin Amurka na yin gaban kanta da kuma yin babakare.

Kowa na ganin cewa, tun lokacin da Donald Trump ya zama shugaban kasar Amurka, gwamnatinsa ta sanar da janyewa daga yarjejeniyoyi ko kuma hukumomi daban-daban, ciki har da yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi, da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta dukkan fannoni, da hukumar UNESCO da kwamitin kula da kare hakkin dan Adam na MDD da sauransu, har ma tana shirin janyewa daga yarjejeniyar cinikin makamai ta MDD. Har wa yau kuma, ta kara sanya haraji kan kayayyakin da take shigowa da su daga wasu abokan cinikinta, ciki har da Sin da tarayyar Turai da Japan da Mexico da Kanada. Babban dalilin da ya sa Amurka ta yi haka shi ne, domin a ganinta, doka da oda da aka kafa bayan yakin duniya na biyu gami da ka'idojin cinikin kasa da kasa na yanzu ba za su iya gamsar da Amurka ba, shi ya sa take keta su in har tana son yin haka, har ma tana da niyyar kawar da su dukka, da zama kasa mai karfin fada a ji ita kadai a duniya.

 

Hakan ya sa mutane fahimtar cewa, manufar "kasar Amurka a matakin farko" da gwamnatin kasar Amurke ke kokarin aiwatar da ita, ma'anarta ita ce sanya moriyar kasar da farko a kan ka'idojin kasa da kasa, don tabbatar da ikonta wanda ya zarce ka'idojin duniya, ta yadda kasar za ta samu damar kiyaye ikonta na danniya wanda ke kan hanyar rushewa. Wannan manufar da kasar Amurka ta gabatar wato "kasar Amurka a matsayin farko" ta yi daidai da tsarin yin gaban kai da matakan nuna fin karfi da kasar Amurka ta dade tana amfani da su, amma ta kara bayyana ra'ayin kasar a fili ba tare da rufa-rufa ba.

Sai dai sakamakon wannan manufar ta "kasar Amurka a matsayin farko" shi ya sanya kasar ta gamu da matsala kafin sauran kasashe. Ga misali, yadda kasar Amurka ta dade da kin cika alkawuran da ta dauka, da yadda ta janye daga kungiyoyi daban daban, sun bata sunan kasar matuka, da raunana moriyar kasar ta tushe. Wani karin maganar kasar Sin na cewa: "Mai gida ba zai ta da hargitsi ba." Amma yanzu kasar Amurka a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki da na soja a duniya, ta kan tsoma baki cikin harkokin gida na kawayenta. Yayin da a sa'i daya ta ce kasashe kawayenta ba su biya kudaden karo-karon aikin soja sosai ba, don haka ta yi barazanar janyewa daga kungiyar tsaro ta NATO. Yadda kasar take tsumulmula ya lalata huldar dake tsakaninta da kawayenta sosai.

A kwanakin nan ne, jakadan kasar Amurka a kungiyar tarayyar Turai ya gargadi kungiyar game da shirinta na asusun tsaro, inda ya ce, ka'idojin da aka tanada za su iya sa kamfanonin kasar Amurka su kasa samun kwangila daga kungiyar, har ma ya yi barazanar daukar matakai na sanya takunkumi. Don haka, kasashen Jamus da Faransa suka yi shelar kafa rundunar sojojin Turai, ta yadda Turai za ta samu 'yancin kanta ta fannin tsaro, wato ba tare da dogara ga kasar Amurka ba.

A sa'i daya kuma, matakan da Amurka ta dauka na sanya haraji shi ma ya kawo wa masu sayayya na kasar illa. Larry Kudlow, shugaban kwamitin kula da harkokin tattalin arziki na fadar White House ya amince da cewa, kamfanonin kasar Amurka ne za su yi hasarori a sakamakon harajin da gwamnati ta kara sanyawa, kamfanonin da kuma su kan sa masu sayen kayansu ne hasarar za ta shafa.

Kididdiga na nuna cewa, sakamakon kara sanya harajin da Amurka ta yi kan kayayyakin kasar Sin, yawan kudi da kasar Amurka ta samu a fannin aikin gona ya ragu da kashi 12 cikin dari a shekarar 2018, hasarar da kasar ta yi a fannin tattalin arziki ta kai dala biliyan 7.8 tun daga bara. Idan aka kara yawan haraji kan kayayyakin da kasar ke shigowa daga kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 250 na kashi 25 cikin 100, da kara karbar haraji kan kayayyakin da ake kera da ingantaccen bakin karfe da karfen goran ruwa, to guraban ayyukan yi a kasar Amurka za su ragu zuwa dubu 934 a ko wace shekara.

 

Duniya a karni na 21 duniya ce da kasashe daban daban ke da makoma ta bai daya, ba zai yiwu ba a sake mayar da al'umma cikin tsarin mulkin mallaka ba. Ko shakka babu aikin kasar Amurka na yin watsi da alhakinta kan duniya, da mugun matakin da ta dauka na kara sanya haraji za su gamu da adawa daga kasashen duniya.

An lura da cewa, ban da kasar Sin dake nuna matsayin ta kan shawarwari a tsakaninta da Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da nuna adawa da matakin kara sanya haraji, ita ma babbar kwamishinan kungiyar EU Cecilia Malmstrom ta bayyana cewa, a kokarin da ake na tinkarar matakin Amurka na yiwuwar kara sanya harajin kwastan kan motocin da take shigowa daga EU, yanzu kungiyarta na tsara takardar jerin sunayen kayayyakin Amurka da su ma za a sanya musu haraji don mayar da martani.

A shawarwarin cinikayya da aka yi tsakanin Japan da Amurka wanda aka kammala a watan jiya, Japan ta ki yarda da bukatun Amurka na soke ko rage yawan harajin amfanin gona da Japan ta sanya. A waje daya kuma, yanzu an kusan kammala shawarwari mafi girma na yin ciniki maras shinge na yankin Asiya da tekun Fasific, wanda Amurka ba ta sa hannu a ciki ba. Ban da wannan kuma a gun taron koli na kungiyar G20 da aka yi a birnin Hamburg na kasar Jamus a watan Yuli na shekarar 2017, an nuna wa Amurka wariya sakamakon ra'ayinta wanda ya saba da na saura. Haka zakila, taron koli na karo na 12 na shugabannin kasashen Asiya da Turai wanda aka yi a watan Oktoba na shekarar 2018 ya ba da sanarwar cewa, dukkansu na goyon bayan yarjejeniyar nukiliyar Iran wadda Amurka ta riga ta janye daga cikinta.

Kamar yadda Sinawa ke cewa, duk wanda ke samun goyon bayan al'umma, zai samu taimako sosai, yayin da wanda ba ya samun irin wannan goyon bayan, ba shakka babu wanda zai taimaka masa. Yanzu duniya na kara dunkulewa waje guda, amma Amurka tana rufe kofarta da ma kebe kanta daga dangi. Dalilin da ya sa hakan shi ne sabo da manufar "mayar da kanta fiye da kowa" da Amurka ke dauka.(Tasallah Amina Murtala Bello Lubabatu Bilkisu Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China