in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shirya taron tattaunawa na kasa da kasa kan yadda za a kara bunkasa shiyoyyin cinikayya marasa shinge
2019-05-15 12:23:09 cri

Bisa labarin da wakilinmu ya samu daga hukumar ingiza cinikayya tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin, an ce, hukumar gwamnatin lardin Hainan zasu yi hadin gwiwar shirya farkon taron tattaunawa na kasa da kasa kan yadda za a inganta bunkasa shiyyoyyin cinikayya marasa shinge a tsakanin rainakun 21 da 22 ga watan Mayun a lardin Hainan. Wannan ne karo na farko da za a a shirya irin wannan taron tattaunawa game da batun bunkasa shiyyoyin cinikayya marasa shinge cikin shekaru 5 ko fiye. Dalilin da yasa za a shirya wannan taron tattaunawa shine, yin kwaskwarima da kirkiro sabbin hanyoyin bunkasa shiyyoyin cinikayya marasa shinge a kasar Sin, da neman sabbin hanyoyin gyara tasoshin teku, inda za a iya yin cinikayya ba tare da shinge ba bisa hakikanin halin da ake ciki a kasar Sin, ta yadda za a iya inganta manufofi da matakan kara bude kofar kasar Sin ga ketare.

Shiyyar cinikayya maras shinge ta kasance kamar wani muhimmin mataki ne da wata kasa ta dauka domin bayyana yadda ita kanta take kokarin bude kofarta ga ketare, da ingiza yin cinikayya cikin 'yanci. Shiyyoyin cinikayya marasa shinge da kasar Sin take gwajin gudanarwa a wasu manyan birane da larduna su ne irin wannan misali. A yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya Talata, Mr. Feng Yaoxiang, direktan sashen ingiza zuba jari na hukumar ingiza cinikayya tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, babban jigon wannan taron tattaunawa shine, "kafa ingantaccen yanayin kasuwanci da yin cinikayya maras shinge". Ya nuna cewa, a yayin taron tattaunawa, mahalarta taron za su tattauna bisa batutuwan "samun damar yin hadin gwiwa wajen bunkasa shiyyar cinikayya maras shinge" da "yadda za a bude kofa domin bunkasa cinikayyar hidimomi a shiyyar cinikayya maras shinge" da dai makamatansu.

"A yayin karamin taron 'Samun damar yin hadin gwiwa wajen bunkasa shiyyar cinikayya maras shinge', mahalarta taron zasu bayar da ra'ayoyinsu kan yadda za a iya bunkasa wata babbar kasuwar cinikayya dake shafar duk duniya, da kafa yanayin kasuwanci ta yanar gizo tsakanin kasa da kasa, da kuma kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a fannin bunkasa shiyyoyin cinikayya marasa shinge a kasashen da shawarar 'ziri daya da hanya daya' ta shafa. Sannan a yayin karamin taro kan yadda za a bude kofa domin bunkasa cinikayyar hidimomi a shiyyar cinikayya maras shinge, za a kara maida hankali kan yadda za a sa ido da bada hidima kan wasu cinikayyar bada hidimomi da basu samu izini ba, da kasuwannin bada hidima da kuma batun bude kofar cinikayyar bada hidima ga ketare baki daya, har ma za a tattauna kan yadda za a kirkiro sabbin ka'idojin bunkasa cinikayyar bada hidima. Bugu da kari, a yayin karamin taron tattaunawa kan yadda za a dauki matakai daban daban wajen bunkasa shiyyoyin cinikayya marasa shinge bisa hakikanin halin da kowace kasa ko kowane wuri yake ciki, mahalarta zasu tattauna game da inganta matakan bunkasa shiyyoyin cinikayya marasa shinge."

Sannan a yayin taron, hukumar ingiza cinikayya tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin zata fitar da "Shawarar Haikou Game Da Bunkasa Shiyyoyin Cinikayya Marasa Shinge", inda za a bada ra'ayoyin 'yan kasuwa da masu tafiyar da masana'antu kan yadda za a kara bunkasa cinikayya da zuba jari da yin hadin gwiwar tattalin arziki, da bunkasa cinikayya ba tare da shinge ba, domin cin gajiyar tattalin arziki da ake bunkasa shi a duk duniya baki daya. Mr. Feng Yaoxiang ya kara da cewa, "Shiyyoyin cinikayya marasa shinge sun kasance kamar ingantaccen dandali ne dake bayyana yadda kasashen duniya suke kokarin kara bude kofofinsu ga ketare. A cikin wadannan shiyyoyi, kowace kasa ta kafa yanayin kasuwanci mafi inganci. Masana'antu zasu iya yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, 'yan kasuwa da masu tafiyar da masana'antu zasu iya yin cikakkiyar mu'amala kamar yadda suke fata tsakaninsu. Sakamakon haka ne, zamu fitar da takardarmu ta bada shawara a yayin wannan taron tattaunawa. Muhimmin dalilin da yasa muka yi haka shine, muna fatan za a kara yin hadin gwiwa a fannonin cinikayya da tattalin arziki, ta yadda za a iya kara bunkasa cinikayya tsakanin kasa da kasa ba tare da shinge ba, da kuma karfafa musaya da kuma koyon ra'ayoyin bangarori daban daban."

An labarta cewa, wannan taron tattaunawa ya jawo hankulan 'yan kasuwa da masu tafiyar da masana'antu na kasa da kasa. Kawo yanzu, sanannun shiyyoyin cinikayya marasa shinge guda 11 da kungiyoyin kasa da kasa 5 da gidajen jakadancin kasashe 17 dake nan kasar Sin, da wakilan masana'antu 11 wadanda suke cikin masana'antu mafi girma guda 500 a duk duniya sun ce, zasu tura wakilansu zuwa taron. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China