in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi gwajin saukar jiragen sama na farko a sabon filin jiragen sama na birnin Beijing
2019-05-13 13:53:24 cri

Da safiyar yau Litinin ne aka gudanar da gwajin saukar jiragen sama guda 4, a matsayin gwajin farko na zirga zirgar jiragen sama, a sabon filin jiragen saman Daxing dake nan birnin Beijing.

Jiragen sama na kamfanonin "China Southern Airlines", da "China Eastern Airlines", da "Air China" da na "Xiamen Airlines" ne suka yi gwajin jiragensu.

A cewar wani kusa a hukumar dake kula da harkokin sufurin jiragen saman kasar Sin Wan Xiangdong, gwajin ya nuna yadda aka karkata hankula ga shirye shiryen tashi da saukar jiragen sama a sabon filin, bayan da aka yi nisa da ayyukan gina abubuwan bukata.

Wan Xiangdong ya kara da cewa, gwajin ya biyo bayan wanda aka yi a ranar 22 ga watan Janairun bana, domin tantance yiwuwar amfani da filin ga jiragen fasinja. Ana dai sa ran fara gwajin jiragen sama masu tafiya nesa da kasa a watan Agusta, kana a fara amfani da filin gadan gadan kafin ranar 30 ga watan Satumba mai zuwa.

Filin tashi da saukar jiragen saman Daxing na da nisan kilomita 46 kudu daga kwaryar birnin Beijing, ana kuma fatan bude shi zai rage cunkoson sufuri a babban filin jiragen saman kasa da kasa na Beijing dake arewa maso gabashin birnin.

Sabon filin jiragen saman dai na tsakanin yankin Daxing da Langfang, sabon yankin dake makwaftaka da lardin Hebei. Filin jiragen zai rika karbar fasinjoji kimanin miliyan 45 duk shekara nan da shekarar 2021, adadin da ake hasashen zai karu zuwa fasinjoji miliyan 72 ya zuwa shekara ta 2025.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China