in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi babban zabe a kasar Afirka ta Kudu
2019-05-09 15:15:15 cri

Jiya Laraba 8 ga wata agogon wurin ne, aka gudanar da babban zabe a duk fadin kasar Afirka ta kudu, zaben da ke gudana bayan shekaru biyar. An kuma kammala jefa kuri'ar zaben da karfe 9 na daren ranar. Yanzu an fara kididdigar kuri'un.

Jiya Laraba ne, aka gudanar da zaben majalisar dokokin tarayya da na jihohin kasar Afirka ta kudu, zabukan dake gudana bayan shekaru biyar. Masu zabe kimanin miliyan 26 ne suka jefa kuri'unsu a tashoshin jefa kuri'a dubu 23 da aka tanada a duk fadin kasar, domin zaben jam'iyyun da suke so. Bisa tsarin kasar, jam'iyyar siyasa da ta samu rabin kujeru a majalisar ce za ta kafa mulkin kasar, yayin da shugaban jam'iyyar kuma zai zama shugaban kasar.

A zaben na wannan karo, jam'iyyun siyasa 48 ne a kasar Afirka ta kudu ke takarar lashe kujeru 400 na majalisar dokokin kasar, amma Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar da Jam'iyyar hamayya ta DA da EFF su ne manyan jam'iyyun dake takara da juna.

A wata tashar jefa kuri'a da ke yankin Fourways na birnin Johannesburg, cibiyar tattalin arzikin kasar, wakilinmu ya gano cewa, masu zabe sun shiga layi ne tun da sassafe, ana kuma gudanar da aikin jefa kuri'a lami lafiya.

Jeffrey Robile, wani mai zabe ya gaya wa wakilinmu cewa, yana goyon bayan Jam'iyyar ANC mai mulkin kasarsa. A ganinsa, tun bayan da Cyril Ramaphosa ya zama shugaban jam'iyyar, farin jinin jam'iyyar ya farfado, Ramaphosa na da kwarewa wajen jagorantar al'ummar kasar don samun kyakkyawar makoma. Ya kara da cewa,

"Ina zaton cewa, zaben na wannan karo zai kyautata makomar kasarmu. Ina jin kauna ganin hadin kai a tsakanin kabilu daban daban dake kasar, lallai al'ummarmu na da hadin kai sosai. Ina da imani a kan Ramaphosa, wanda a ganina shi ne mutumin da ya fi cancanta wajen jagorantar Afirka ta kudu don kara samun ci gaba, ganin yadda ya riga ya kyautata kasar sosai, kuma zai ci gaba da yin kwaskwarima a kasar. Mun yi imani da shi, tabbas zai kawo wa kasarmu sauye-sauye, da ma bai wa al'ummarmu kwarin gwiwa kan fatanmu na kawo sa alheri ga makomar kasarmu."

Amma a wani bangare, wasu masu zabe sun nuna rashin jin dadi ga yadda Jam'iyyar ANC ke tafiyar da harkokin kasar. Wata mai zabe wadda ba ta son a fayyace sunanta ta ce, ta zabi jam'iyyar hamayya ce, tare da fatan jam'iyyar za ta kawo gyare-gyare kamar yadda take fata. Ta ce,

"Ina ganin cewa, a cikin shekaru 25 da suka wuce, babu abin da ya canja a kasar. Ina fatan za a samu sakamako na daban a wannan zaben, domin yaranmu su amfana."

Ra'ayin jama'a na nuna cewa, ko da yake Jam'iyyar ANC ta samar da ci gaba a fannonin kyautata zaman rayuwar jama'a, da ma bunkasar tattalin arziki a cikin shekaru 25 da suka gabata a matsayinta na jam'iyya mai mulkin kasar, amma an samu 'yan sabani da kalubaloli masu tarin yawa.

A jiya da safe ne, Ramaphosa ya bayyana wa magoyansa ta kafofin watsa labarai a wata tashar jefa kuri'a, cewar lallai jam'iyyarsa ta yi kurakurai, amma yanzu ta fahimci hakan da nufin kawo gyara, kuma ta nemi gafarar jama'a. Don haka Ramaphosa ya yi kira ga jama'a da su sake nuna imani ga jam'iyyar ANC. Yana mai cewa,

"Ina fatan al'ummarmu za su ci gaba da goyon bayan jam'iyyar ANC, ganin yadda zaman rayuwar al'ummar ya kyauta sosai bisa jagorancinta a cikin shekaru 25 da suka wuce. Za mu ci gaba da bunkasa tattalin arziki, da jawo jari, a kokarin biyan bukatun jama'a."

Binciken ra'ayin jama'a na nuna cewa, jam'iyyar ANC za ta samu kaso 60 na dukkan kuri'un da aka jefa a kasar, don haka babu shakku za ta samu nasara a zaben. Amma yadda za a warware matsalolin da Afirka ta kudu ke fuskanta a fannin samun ci gaba, zai jarraba kwarewar jam'iyyar, lamarin da zai yi babban tasiri ga imanin da jama'a ke nuna mata da ma babban zabe mai zuwa bayan shekaru biyar.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China