in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankuna dake cikin shawarar BRI sun kasance tamkar kungiyar tattalin arziki mafi girma ta biyu a duniya
2019-05-08 16:53:31 cri

Tun bayan da aka shiga watan Mayu, wasu rahotannin nazari biyu da aka wallafa game da yadda ake bunkasa shawarar "ziri daya da hanya daya", wato BRI a takaice a Turanci sun jawo hankalin al'umma sosai.

Daya daga cikinsu shi ne "Rahoto game da alkaluman jari da cinikayya da aka yi karkashin shawarar 'ziri daya da hanya daya' " da wasu hukumomin ba da shawarwari na kasar Sin da na waje wadanda suke karkashin jagorancin cibiyar musayar tattalin arzikin kasa da kasa ta kasar Sin suka fitar a jiya Talata a nan Beijing. A cikin wannan rahoton, an nazarci alkaluman da MDD ta fitar, wanda ke nuna cewa, ya zuwa yanzu, yawan tattalin arzikin yankunan dake alaka da shawarar "ziri daya da hanya daya" ya wuce na yankin yin cinikayya cikin 'yanci na arewacin Amurka, inda ya zama na biyu mafi girma a duk duniya biyo bayan yankin kawancen kasashen Turai wato EU. Daya rahoton da hukumar Moody's, wato hukumar dake tantance matsayin hukumomi ko kamfanonin duniya ta fitar a kwanan baya, ta bayyana cewa, bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, an samar da muhimman kayayyakin more rayuwar al'ummomi a kasashe da yankunan da shawarar ta shafa, har ma ta bayar da muhimmiyar gudummawa ga bunkasar tattalin arzikin wadannan kasashe da yankuna a nan gaba.

A game da alkaluman zuba jari da cinikayya a kasashen da suke aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" kuwa, rahoton ya bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2017, adadin cinikayyar da wadannan kasashe suka shiga a fadin duniya ya karu zuwa kaso 55.2 bisa dari, a sa'i daya kuma, kason adadin cinikayyar dake tsakaninsu a cikin daukacin cinikayyar kasa da kasa shi ma ya karu zuwa kaso 13.4 bisa dari, adadin da ya zarta na yankin cinikayya maras shinge na arewacin Amurka, inda ya yi daidai da kaso 65 bisa dari na adadin cinikayyar dake tsakanin kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai wato EU.

Hakika karuwar cinikayya da zuba jari shi ne muhimmin dalilin da ya sa aka samu farfadowar tattalin arzikin duniya, rahoton ya kuma bayyana cikakkun alkaluma da ke nuna cewa, aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" ya taimaka wajen bunkasar harkokin cinikayya da zuba jari a kasashe da yankunan da suka shiga shawarar, lamarin da ba ma kawai ya ciyar da tattalin arzikin kasashen da yankunan gaba ba, har ma ya taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya baki daya.

Wannan tsokaci ya tabbatar da gaskiyar da wani rahoton da babban kamfanin nazarin tattalin arziki na Moody's ya gabatar. An kuma gabatar da wannan rahoton, bayan da aka yi nazari kan makomar tattalin arziki na wasu kasashe 12 da hadarin da suke fuskanta a kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a kasuwanninsu, inda aka bayyana cewa, wasu kasashe da suka hada da Pakistan, Mongolia, Khazakstan, da Cambodia, sun samu damar samun mafi yawan karuwar tattalin arziki bayan shiga tsarin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya".

A karshen watan da ya gabata, tsohon shugaban kasar Khazakstan, Nursultan Nazarbayev, ya zo birnin Beijing na kasar Sin don halartar dandalin tattaunawar manyan jami'ai game da hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" karo na 2, inda ya bayyana amincewarsa kan dabarar kasar Sin ta neman hade kayayyakin more rayuwar jama'a, ta hanyar amfani da karin maganar Sinawa dake cewa "in ana son a samu wadata, sai an fara gina hanyoyi."

Daukacin al'ummar Sinawa sun san da wannan karin magana, wadda ta bayyana muhimmancin kayayyakin more rayuwa, musamman ma fannin sufuri, ga ci gaban tattalin arzikin duk wani yanki. Albarkacin shawarar "Ziri Daya da Hanya daya", wannan karin maganar ta yadu zuwa kasashe da yankuna daban daban na duniya.

A yayin bikin bude taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" da aka gudanar a karo na farko a shekaru biyu da suka wuce, babban sakataren MDD, Antonio Gutterres ya bayyana cewa, "Sinawa kan ce, in ana son a samu wadata, sai an fara gina hanyoyi". MDD na son hada gwiwa da kasar Sin wajen gina wannan hanyar, don samun dauwamammen ci gaba, ta yadda daukacin al'umma za ta amfana."

Hanyar da ya ambata a hakika ta wuce maganar hanyoyin mota da layukan dogo, har ma ta hada da hadin gwiwa da juna a fannonin musayar kayayyaki da kudaden jari da fasahohi da kuma al'adu. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a kwanakin baya, y ace, "abu mai muhimmanci wajen raya 'ziri daya da hanya daya' shi ne hadewa da juna. Ya kamata mu raya huldar abokantaka ta hadewa da juna, ta yadda za a tabbatar da samun ci gaban juna."

Sassa daban daban da suka shiga ayyukan raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" suna kokarin hada kai don zama wata kungiyar raya tattalin arzikin duniya game da shawarar mai salon bude kofa, yin hakuri, mu'amala, neman dauwamammen ci gaba da mai da hankali kan jama'a da dai sauransu. Yayin da aka turbar neman ci gaba mai inganci, ana sa ran kungiyar tattalin arzikin dake da manufar yin shawarwari ta hanyar hada kai, da more nasarorin da aka samu tare, za ta taka sabuwar rawa kan ci gaban tattalin arzikin kasashensu da na duniya baki daya. (Sanusi, Jamila, Bello, Lubabatu, Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China