in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dalilin da ya sa kasashen Afirka ke bukatar zuba jari a bangaren ababen more rayuwa
2019-05-08 13:26:42 cri

Masanan na da yakinin cewa, zuba jari a bangaren ababen more rayuwa, na kara habaka kasuwanci da jan hankalin masu zuba jari ga sauran bangarorin tattalin arziki. Baya ga haka, ababen more rayuwa na kara ingiza kirkire-kirkire da habaka ayyukan masana'antu da rage kudaden da ake kashewa wajen sayen kayayyaki da saukaka cinikayyar kayayyaki da hidimomi tare kuma da yayata basira.

Masanan sun kara da cewa, ayyuka yadda ya kamata na ababen more rayuwa, kamar tituna da tsarin sufurin layin dogo da tasoshin jiragen ruwa da makamashi da filayen jiragen sama ake bukata wajen dunkulewar tattalin arziki da sauran kasashen duniya.

An kuma lura cewa, har yanzu, kasashe da dama na Afrika na fuskantar gibi tsakanin birane da kauyuka da kuma tsakanin mutane da damarmaki.

Chalwa Chiselwa, mai shekaru 43 mazauniyar kauyen Kabeleka dake wajen birnin Lusaka na Zambia, na cike da farin cikin samun sabbin ababen more rayuwar da ba ta ci gajiyarsu ba da kuruciyarta.

Ta ce abun burgewa ne ganin yanzu babu bukatar zuwa birni don sayen kananan abubuwa kamar sabulu ko suga, saboda a yanzu suna da shagunan dake shake da kayayyakin da suke bukata a kauyensu. Ta kara da cewa, yanzu suna da makarantu da cibiyoyin lafiya a cikin kauyen, wanda kuma suke aiki yadda ya kamata, ga kuma tsaftataccen ruwan sha da wutar lantarki da kuma tituna masu kyau.

Chalwa mai 'yaya 5 na jin dadin ganin 'yayanta 4 na zuwa makaranta kuma ba sa fuskantar kalubale a bangaren samun ilimi da kulawar lafiya, lamarin da ya sha bamban da lokacin da take tasowa.

Ta ce zuwa makaranta a kullum babban aiki ne saboda sai an tafiya mai nisa da kafa. Kuma a lokacin babu tituna masu kyau, a don haka, yara da dama suka daina zuwa makaranta, abun da ya haifar da matsaloli kamar auren wuri da karuwar jahilci.

Ta ce rayuwa ta kyautata yanzu, kuma kaura zuwa birni ya zama abu na zabi, saboda yanzu suna da kusan duk abun da suke bukata a kauyansu. Yanzu akwai makarantun gwamnati da cibiyoyin lafiya a Kabeleka, kuma mazauna kauyen na samun ruwan sha mai tsafta daga rijiyoyin burtsatsai, maimakon koguna dake cike da kwayoyin cuta.

A cewarta, da dukkan kauyukan Zambia za su samu wutar lantarki da ruwan sha mai tsafta da cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu da kuma hanyoyin sadarwa na zamani, to za a samu gagarumar raguwar adadin mutanen dake kaura zuwa birni, saboda wadancan abubuwan ne jan hankalinsu.

Labarin Chalwa ya nuna cewa, ababen more rayuwa na da muhimmanci ga gaggauta ci gaban tattalin arziki da rage fatara. Ya kuma nuna cewa, raya ababen more rayuwa ita ce jigon samar da ci gaba mai dorewa da kowa zai ci gajiya.

Caesar Cheelo, jami'in bincike kan harkokin tattalin arziki na cibiyar bincike da tsara manufofi ta Zambia Institute for Policy Analysis and Research (ZIPAR), ya ce ya kamata a gane cewa, raya ababen more rayuwa ita ce jigon cimma kusan dukkan burikan samun ci gaba. Ya ce kasashen da suka samu ci gaban tattalin arziki, sun zuba jari sosai a kan ayyukan more rayuwa.

Caesar Cheelo ya kara da cewa, dimbin jarin da kasar Sin ke zubawa a bangaren ayyukan raya kasa, ya taimaka mata wajen zama mai karfin tattalin arziki.

A cewar bankin raya nahiyar Afrika AFDB, raya ababen more rayuwa a Afrika na da matukar muhimmanci wajen inganta bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar nahiyar. Kana tana ba da gudunmuwa ga bunkasa kwarewar jama'a da rage fatara da kuma kai wa ga cimma muradun ci gaba masu dorewa.

Wani rahoto da bankin ya fitar a baya-bayan nan, ya ce zuba jari a bangeren kayayyakin more rayuwa shi ya haifar da sama da rabin ci gaban tattalin arzikin da aka samu a Afrika, kuma yana da damar ba da karin gudunmuwa.

Shi kuwa bankin duniya ya yi kiyasin cewa, kudin shigar da kowanne dan kasa zai samu a yankin kudu da hamadar Sahara, zai karu da kaso 1.7 bisa dari a shekara, idan yankin zai cike gibin da yake fuskanta na kayayyakin more rayuwa, wanda kuma zai kara samar da ci gaba na bai daya tare kuma da rage fatara a fadin nahiyar.

Har ila yau, wani rahoton kamfanin Deloitte na Birtaniya mai ba da hidimar kwararru ya nuna cewa, kasashe masu tasowa dake ba da kaso 30 bisa dari na alkalumansu na GDP ga ayyukan more rayuwa na daga cikin kasashen da suka samu ci gaba cikin sauri a duniya.

Rahoton ya kara da cewa, cikin shekaru 20 da suka gabata, kasar Sin ta taimaka wajen samar da kudaden ginin ababen more rayuwa da nahiyar Afrika ke bukata, kuma a yanzu, ita ce kasa daya tilo da ta fi kowacce a duniya samar da kudaden aiwatar da ababen more rayuwa a nahiyar, inda take samar da kudin aiwatar da aiki 1 cikin ayyuka biyar tare da aiwatar da 1 cikin ayyuka 3. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China