Masanin Burtaniya kan harkokin kasar Sin: Ya zama dole kasashen yammaci su gano wata hanyar cudanya da kasar Sin
Masanin kasar Burtaniya kan harkokin kasar Sin, wanda kuma shi ne babban manazarci a jami’ar Cambridge, Mr. Martin Jacques a kwanan baya ya rubuta cewa, dole ne kasashen yammacin duniya, musamman ma Amurka su gano wata hanyar cudanya da kasar Sin, a maimakon su ci gaba da nuna girman kai. Ya ce kamata ya yi Amurka ta saba da sabon yanayin da duniya ke ciki, kuma ta mutunta kasar Sin a matsayin abokiyar takararta, ta yadda za ta gano wata sabuwar hanyar yin hadin gwiwa da kasar Sin da kuma fuskantarta.
A sharhinsa mai taken “What China Will Be Like as a Great Power”, Martin Jacques ya ce, “Babbar matsalar da kasashen yamma suke fuskanta ita ce rashin fahimtar kasar Sin da zurfin tunaninmu, wato a ganinmu, kasashen yamma na iya wakiltar kowa, kuma salon zamani daya a duniya, wato irin salon zamani na kasashen yamma.” Sai dai ra’ayin bai iya zaunawa da gindinsa ba, sabo da ba kawai sauye-sauye na faruwa a kasar Sin ba, kasashe masu tasowa da dama ne suka bambanta da kasashen yamma ta fannonin tarihi da siyasa da kuma al’adu. A cikin irin wannan hali ne, ya zama dole kasashen yamma su yi kokarin fahimtar bambancin da ke tsakaninsu da kasar ta Sin. (Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku