in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda sun tabbatar da rasuwar mutane 10 yayin wani hari a Zamfara
2019-05-07 20:56:08 cri
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da rasuwar mutane 10, yayin wani harin 'yan bindiga a kauyen Dungurgu dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Kakakin rundunar reshen jihar Zamfara Muhammed Shehu ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa yanzu haka an tsaurara tsaro a yankin, tun bayan aukuwar wannan hari na ranar Asabar. Ko da yake bai yi karin haske game da hakan ba, amma ya ce akwai karin wasu mutanen da suka jikkata yayin harin.

Wasu al'ummar yankin sun bayyana cewa, harin na ranar Asabar ya auku ne yayin da al'ummar kauyen ke halartar wani bikin suna.

Dagacin kauyen na Dungurgu Hussaini Umar, ya ce maharan sun bullo ne ta wani daji a kan Babura, inda nan take suka bude wuta, suka tarwatsa taron mutanen dake bikin suna.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China