in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takunkuman da Amurka ta kakabawa Cuba da Venezuela da Iran sun sabawa dokokin duniya, in ji Idriss Jazairy
2019-05-07 20:22:54 cri
Wakilin musamman na MDD mai lura da mummunan tasiri da takunkumai ke haifarwa Idriss Jazairy, ya ce matsin lamba bisa radin kai da Amurka ke yiwa kasashen Cuba, da Venezuela, da Iran, ya sabawa kudurorin kare hakkokin bil Adama, da ma manufofin zamantakewar kasashen duniya.

Idriss Jazairy, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a Litinin din nan, yana mai cewa kakaba takunkumin tattalin arziki domin cimma burin siyasa, ya yi hannun riga da ka'idojin kare hakkin bil Adama. Ya ce irin wadannan matakai na iya ingiza fadawa masifu da za su haifar da bukatun jin kai marasa iyaka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China