in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin: Sin na da sahihiyar zuci wajen ci gaba da yin shawarwari da Amurka kan harkokin tattalin arziki da cinikayya
2019-05-07 18:54:42 cri
A yau Talata ne kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, mutunta juna da kuma zaman daidaito da juna, su ne sharadi da tushen cimma yarjejeniya, kuma kara sanya haraji ba zai taimaka ga warware matsala ba. Ya ce Sin ba za ta gujewa duk wata matsala ba, kuma tana da sahihiyar zuci wajen ci gaba da yin shawarwari da Amurka, kan harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Bisa goron gayyatar da wakilin kasar Amurka kan harkokin cinikayya Robert Lighthizer, da ma sakataren kudin kasar Steven Mnuchin, suka ba shi, Mr. Liu He, mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar Sin kuma shugaban tawagar kasar Sin kan shawarwarin tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka zai ziyarci Amurka tsakanin ranakun 9 da 10 ga wata, domin yin shawarwarin tattalin arziki da cinikayya karo na 11 tare da bangaren Amurka. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China