in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana shirin kara rufe kananan wuraren hakar kwal
2019-05-07 14:12:38 cri

Wata muhimmiyar takarda da hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta fitar, na nuna cewa, kasar tana shirin rufe karin kananan wuraren hakar kwal, da ake hako kasa da tan 300,000 zuwa kasa da tan 800 a shekara nan da shekarar 2021, saboda dalilai na tsaro.

Baya ga wannan mataki, mahukuntan kasar Sin, za su taimakawa wuraren hakar ma'adinai dake bunkasa ma'adinai da kula da ingancin aiki don kara yawan albarkatun da suke hakowa.

Bugu da kari, muddin ana bukatar magance matsaloli, kamar hako kwal fiye da kima da rashin ingantaccen tsaro, 'yan shekarun nan, kasar Sin ta tsaurara sabbin matakai a bangaren hakar kwal da daina ba da lasisi ga sabbin wuraren hako kwal, har sai an rufe wani adadi kamar yadda gwamnati ta bukata.

Takardar ta kuma bayyana cewa, gwamnati za ta mayar da hankali kan shirin maye gurbin wuraren hakar kwal marasa inganci da aka amince. Alkaluma da kungiyar masu hakar kwal ta kasar Sin ta fitar a baya, sun nuna cewa, a karshen shekarar 2018, adadin wuraren hakar kwal a kasar sun ragu zuwa 5,800 kuma matsakaicin karfinsu na hakar kwal ya karu zuwa kimanin tan 920,000 a shekara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China