



Filin hakar kwal na Haizhou da ke birnin Fuxin na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin ya taba zama filin hakar kwal mafi girma a Asiya, wanda kuma ya ba da gudummowa sosai wajen raya tattalin arzikin kasar. Amma yanzu ya zama wurin shan iska ga mazauna wurin.