in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsare dan uwan tsohon shugaban Aljeria da wasu shugabannin hukumar tattara bayanan sirri
2019-05-05 16:29:54 cri
Hukumomin tsaro a Aljeria, sun tsare wasu tsoffin manyan jami'an hukumomin tattara bayanan sirri na kasar a jiya Asabar.

Kafar yada labarai ta TSA ta kasar, ta wallafa a shafinta na website cewa, wasu majiyoyoyi daga hukumomin tsaron sun ce Jami'an da aka tsare sun hada tsoffin shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri wato Mohamed Medien da aka fi sani da Toufik da Bachir Tartag, da kuma Said Bouteflika, dan uwan tsohon shugaban kasar, Abdelaziz Bouteflika.

Shugaban sojin kasa na kasar, Ahmed Gaid Salah, ya zargi jami'an 3 da yi wa rundunar soji da kasar zagon kasa, ta hanyar hana zanga-zangar neman sauyin gwamnati da ta barke a kasar.

Tun daga ranar 22 ga watan Fabrerun bana, jama'a ke zanga-zanga a fadin kasar, suna masu neman sauyin gwamnati.

Rundunar sojin ta yi alkawarin cika burin jama'ar kasar, inda aka kaddamar da tsare manyan jami'an gwamnati da na soji da kuma 'yan kasuwa da ake zargi da laifukan cin hanci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China