in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na daukar matakan kara bude kofar sassan hada-hadar kudi bisa shirin da ta tsara
2019-05-03 17:19:09 cri




A kwanan baya ne shugaban hukumar sa ido kan harkokin bankuna da na inshora Mr. Guo Shuqing ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba, kasar Sin za ta kara daukar wasu sabbin matakai 12, don kara bude harkokin bankuna da na inshora na kasar ga kasashen ketare.

Wadannan sabbin matakai sun biyo bayan wasu matakai 15 da kasar ta Sin ta dauka a watan Afrilun bara, a wani kokari na kara bude harkokin bankuna da inshora na kasar ga ketare, kuma babu shakka, za su kara bude kasuwar bankuna da inshora ta kasar ga ketare, tare da inganta yanayin hada-hadar kudi na kasar, ta yadda za a ba masu jarin waje kwarin gwiwar shiga harkokin hada-hadar kudi na kasar.

 

Harkokin hada-hadar kudi tamkar inji ne na bunkasuwar tattalin arzikin wata kasa. Tun bayan da aka gabatar da kara bude kofofin kasar Sin daga dukkan fannoni, a yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar da ya gudana a shekarar 2017, yayin taron dandalin harkokin Asiya na Bo'ao da aka yi a shekarar 2018 kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana wasu muhimman matakai da za a dauka ta fannoni hudu, don kara bude kofar kasar, ciki har da fannin hada-hadar kudi.

Rahoton aikin gwamnati da kasar Sin ta gabatar a wannan shekara ma ya bayyana muhimmancin tabbatar da matakan kara bude kofofin kasar Sin da suka shafi hada-hadar kudi da ma sauran sana'o'i. Wato ke nan sannu a hankali, kasar Sin na ta bude harkokin hada-hadar kudinta ga ketare bisa ga shirin da ta tsara.

Idan an yi la'akari da wadannan matakai 12 da aka dauka a wannan karo, za a gane cewa, na farko, matakan sun jaddada muhimmancin samar da daidaito a tsakanin jarin gida da na baki. Misali, an daina kayyade kason hannayen jarin na bankin kasuwancin kasar Sin da wani bankin gida da kuma banki mai jarin waje ke iya rikewa. A sa'i daya, an saukaka ka'idojin kafa kamfanonin hada-hadar kudi ga hukumomin hada-hadar kudi na kasar Sin da na ketare, matakin da ya samar da yanayi na daidaito a tsakanin hukumomin hada-hadar kudi na gida da na waje, wanda kuma ya dace da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa da aka zartas ba da jimawa ba.

Na biyu kuma, matakan sun saukaka ka'idojin shiga kasuwar kasar Sin ga hukumomin hada-hadar kudi masu jarin waje, wato an daina kayyade hukumomin hada-hadar kudi masu jarin baki da ke son shiga kasuwar kasar Sin kan yawan kadarorinsu, kuma hakan na iya kara janyo hukomomi masu jarin waje kanana, amma masu inganci, su gudanar da harkokinsu a kasar Sin, kuma a sa'i daya, zai sa kaimi ga kananan hukumomin hada-hadar kudi na kasar Sin da su yi ta inganta harkokinsu.

Na uku, matakan sun fadada fannonin da hukumomin hada-hadar kudi masu jarin baki da ke iya gudanar da harkokinsu. Misali, an amince da bankuna masu jarin baki su gudanar da harkokin da suka shafi kudin kasar Sin RMB, wato ke nan an ba bankunan dama daidai da bankuna na gida kafin a amince da su shiga kasuwar kasar Sin, kuma hakan na iya habaka harkokin da suke iya gudanarwa a kasar Sin.

Bayan shekaru 40 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida, da kuma bude kofa ga ketare, kasar ta cimma nasarorin a zo a gani wajen inganta tsarin harkokin hada-hadar kudi na kasar, kuma ta kafa tsarin bankuna da na inshora da ke da hannayen jari na gwamnati, da masu zaman kansu na kasar, da kuma na baki 'yan kasuwa, daga cikinsu kuma, yawan jarin da baki suka zuba a harkokin bankuna da na inshora na kasar Sin sun kai kaso 1.64% da kuma kaso 6.36%.

Duk da haka, yadda kasar Sin ke bude harkokin hada-hadar kudinta ga baki bai cancanci matsayinta na kasa mai ci gaban tattalin arziki ta biyu a duniya ba, kuma akwai damar kara bude kofarta. Kuma kara bude kofar kasar ga ketare zai iya biyan bukatun bunkasuwar harkokin hada-hadar kudi a kasar cikin dogon lokaci.

A gun taron kolin dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya da aka gudanar kwanan baya a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da matakai biyar na kara bude kofar kasar, ciki har da shigar da jarin baki zuwa karin fannoni, wanda ya kasance muhimmiyar dama ga hukumomin hada-hadar kudi na kasar Sin, haka kuma dama ce ga hukumomi masu jarin baki da ke son shiga kasuwar kasar Sin, da ma wadanda tuni suka shiga kasuwar. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China