in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan kara bude kofa da kasar Sin ke aiwatarwa za su bunkasa sassan hada-hadar bankuna da na inshora
2019-05-03 15:31:10 cri

Hukumar CBIRC mai lura da harkokin bankuna da inshora ta kasar Sin, ta yi hasashen irin nasarar da kasar za ta samu, a fannin fadada hada hadar zuba jari, da harkokin gudanarwa ga baki 'yan kasashen waje, masu niyyar zuba jari a fannonin cinikayya daban daban, duba da yadda ake daukar sabbin matakai na bude sashen ga masu sha'awar zuba jari.

Da yake karin haske game da wannan batu a ranar Laraba, shugaban hukumar ta CBIRC Guo Shuqing, ya ce ana daf da kaddamar da karin wasu sabbin dokoki 12 masu nasaba da hakan, bayan tantance sahihancin su.

Shi ma a nasa tsokaci, kakakin hukumar Xiao Yuanqi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, aiwatar da sabbin dokokin, zai karfafa gwiwar masu zuba jari, su kara shiga sashen inganta hada hadar cinikayya a sassa masu yawa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China