in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bukatar sa hannun sassa daban daban wajen raya "ziri daya da hanya daya", in ji masana
2019-05-01 17:27:30 cri





Kwanan baya, an rufe taron kolin dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu, kuma kawo yanzu, kasashe sama da 120 da kuma kungiyoyin duniya fiye da 20 sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa tare da kasar Sin. Masana na gida da kuma na waje suna ganin cewa, baya ga sassan gwamnati da hukumomi, ana kuma bukatar sassa masu zaman kansu, su sa hannunsu aikin raya "ziri daya da hanya daya".

Wani abin da ya jawo hankalin al'umma shi ne taron masu masana'antu da ya gudana a gefen taron kolin, taron da ya samar da sabon dandalin da kuma damar yin hadin gwiwa ga 'yan kasuwa da kungiyoyin duniya da kuma wakilan hukumomi daban daban da suka zo daga kasashe da shiyyoyi sama da 80. An ce, yarjejeniyar hadin gwiwa da aka cimma a wannan karo a tsakanin kamfanonin kasar Sin da kuma na ketare ta zarce dalar Amurka biliyan 64. Daidai kamar yadda Madam Arancha Gozalez Laya, darektar zartaswa ta cibiyar cinikayyar kasa da kasa ta fada, sassan gwamnati ba su kadai za su iya warware dukkanin kalubale da matsalolin da ake fuskanta wajen raya shawarar "ziri daya da hanya daya" ba, ana kuma bukatar sassa masu zaman kansu su ba da nasu taimako da goyon baya. Ta ce, "Shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da damammaki, musamman ga kasashe masu tasowa. Misali, cinikin da ke tsakanin kasashe masu tasowa ya kai kaso 15% na cinikayyar duniya a shekaru 10 da suka wuce, amma ga shi yanzu ya wuce rabi. Yadda kasa da kasa su kara hadewa da juna ta fannin manyan ayyuka, ya samar wa sassa masu zaman kansu damar yin ciniki. Ban da haka, mun cimma yarjejeniyoyin abokantaka, mun kuma kara tuntubar juna ta fannin tsara manufofi da ma yin kokarin kawar da shingayen ciniki da sa kaimin hadin gwiwar kudi."

A gun taron koli na wannan karo, kasashe da kungiyoyin duniya sun cimma yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da 100 da suka shafi zirga-zirga, da haraji, da ciniki da kimiyya da fasaha, da al'adu da kwararru da kuma kafofin yada labarai. Ding Yifan, babban manazarci a cibiyar nazarin manufofin kasa karkashin jami'ar Tsinghua ta kasar Sin ya bayyana cewa, shirye-shiryen da aka aiwatar za su haifar da karin damammaki na yin hadin gwiwa, ya ce, "Yarjejeniyoyin za su kawo sabbin jari da kuma hadin gwiwa bayan da aka tabbatar da su. Don haka, 'ziri daya da hanya daya' aiki ne da za a gudanar a cikin wani dogon lokaci. Sabo da shawarar ta kasance wani ginshiki wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, wanda a zahiri dai ba za a iya kammala shi cikin yini guda ba."

Tun bayan da aka gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", an gudanar da shirye-shirye da dama yadda ya kamata, ciki har da aikin gina layin dogo a tsakanin kasar Sin da ta Laos, da kuma tsakanin Sin da Thailand. Baya ga haka, akwai tashar ruwa ta Gwadar da ta Hambantota. Daga shekarar 2013 zuwa ta 2018, yawan cinikin kayayyaki da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen da "ziri daya da hanya daya" suka ratsa ya zarce dalar Amurka triliyan shida. Baya ga haka, kasar Sin ta kuma cimma shirin musaya kudade a tsakaninta da kasashe sama da 20 da "ziri daya da hanya daya" suka shafa. A game da wannan, Xu Hongcai, mataimakin darektan sashen kula da manufofin tattalin arziki karkashin kwamitin nazarin kimiyyar manufofi na kasar Sin ya bayyana cewa, tsintsiya madaurinki guda, yadda karin kasashe suka amince da shawarar zai taimaka ga inganta hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar, ya ce, "Tsintsiya madaurinki guda, kofa a bude take ga duk wanda ke sha'awar shiga ayyukan raya shawarar, amma ba a tilastawa wani ko wata su shiga ayyukan ba. Kasar Sin a nata bangaren na kokarin shiga ayyuka, amma ba wai ita ke kula da kome da kome ba. Za ta fara ne da gudanar da aikinta, wato ta kara yi wa tsarinta kwaskwarima ta hanyar kara bude kofarta. A sa'i daya kuma, za ta habaka hadin gwiwarta da kasa da kasa, a kokarin cimma sabon ci gaba a wasu muhimman fannoni." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China